SiyasaAfirka
Mulkin mallaka: Sarkin Ashanti ya baje kolin kayan tarihi
May 1, 2024Talla
Sarkin Ashanti Otumfuo Osei Tutu II ya tsara bikin baje kolin kayayyakin tarihin ne a fadar Manhyia da ke birnin Kumasi, domin tunawa da dakarun Ashanti da suka kwanta dama a lokacin yaki da mulkin mallaka a 1874.
Karin bayani: Ghana ta bukaci hadin kai don neman diyyar mulkin mallaka
Tun da farko gidajen adana kayan tarihin Burtaniya ciki har da ''British Museum'' sun amince da mika takubban zinare 32 da wasu kayayyakin na alfarma ga masarautar ta Ashanti.
Baje kolin kayayyakin na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen Turai da Amurka ciki har da Faransa da Jamus da Portugal ke fuskantar matsin lamba na dawo da kayan tarihin da suka wawushe a lokacin mulkin mallaka.